Aliyu muhammad sadisu
Yüklə 328.38 Kb.
səhifə1/3
tarix25.04.2016
ölçüsü328.38 Kb.
  1   2   3Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa
Wallafar:

ALIYU MUHAMMAD SADISU
Wanda ya duba:
Attahiru Bala Dukku

السبع الموبقات

تأليف

علي محمد سادسمراجعة: الطاهر بلا دكو

بسم الله الرحمن الرحيم

Gabatarwa.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halitta Annabi Muhammad  da iyalansa da sahabbansa baki daya.

Wannan littafi ya kunshi bayani ne akan abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah-Tsira da aminncin Allah su tabbata a gare shi- yace masu halakarwa ne.

Lalle dukkanin abinda Ma'aikin Allah  ya ce 'Abu kaza mai halakarwane', To lalle ya kamata mutum musulmi ya yi kokarin sanin wannan abin, tun da sauran nunfashinshi. Ma'aikin Allah- Tsira da aminncin Allah su tabbata a gare shi- Ya ce:

((اِجْتَنِبُواْ اَلسَّبْعَ اَلْمُوبِقَاتِ، قَالُواْ يَا رَسُولَ اَللهِ وَمَا هِيَ؟ قَالَ: اَلشِّرْكُ بِاللهِ، وَالسِّحْرُ، وَقَتْلُ اَلنَّفْسِ اَلَّتِي حَرَّمَ اَللهُ إِلاَّ بِالْحَقِّ، وَأَكْلُ اَلرِّبَا، وَأَكْلُ مَالِ اَلْيَتِيمِ، وَالتَّوَلِّي يَوْمَ اَلزَّحْفِ، وَقَذْفُ اَلْمُحْصَنَاتِ اَلْغَافِلاَتِ اَلْمُؤْمِنَاتِ)). رواه البخاري ومسلم.
Ma’ana: "Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa! (Sai Sahabban shi -Allah ya kara musu yarda suka ce) 'Wadanne abubuwane wadannan ya Ma'aikin Allah? Sai Ma'aikin Allah- Tsira da aminncin Allah su tabbata a gare shi- Ya ce: "Shirka da Allah, da Asiri da Kashe rai da Allah ya haramta a kashe ta ba tare da hakki ba, da Cin Riba da cin Dukiyar Maraya da Ja-da-baya lokacin gumurzu, da Yiwa mace mumina wacce ta kame kanta (bata san ya ake barna ba) mutum ya yi wa irin wannan macan kazafi."Bukhari ya ruwaito wannan hadisi a wurare da dama a cikin littafinsa, haka ma Muslim ya ruwaito shi.

To wadannan fa sune abubuwa bakwaidin da ma'aikin Allah -Tsira da aminncin Allah su tabbata a gare shi- ya gargadi wannan al'umma, yace ku yi nesa da su kada ku kuskura ku yi kusa da su.

Kenan wannan littafi sharhi ne na wannan hadisin, wadannan abubuwa bakwai su muke fatan zamu yi bayaninsu daya bayan daya da yardar Allah.

Littafin yana kunshe ne da babi guda bakwai, kowanne babi yana kunshe da bayanin abu guda cikin wadannan abubuwa guda bakwai, muna rokon Shi da sunayanSa kyawawa da siffofinshi madaukaka da ya yi mana jagora.Mawallafi.

Aliyu Muhammad Sadisu,

Minna, Nigeria.aliyusadis@gmail.com

Babi Na Farko: Shirka Da Allah
Abu Na Farko: Shirka da Allah.

Itace 'hada bautar Allah da wani' wannan ya nuna cewa bautawa Allah Shi kadai, shine abinda yake daidai, amma hada Allah da wani, bai taba halatta.

Wannan ya sa Allah madaukakin sarki ya dinga turo Annabawa da Manzanni domin su tabbatar da tsan-tsar tauhidi, haka kuma Annabawan da Manzannin suka tsaya tsayin daka domin tabbatar da sun isar da wannan aike da aka yi musu, muna shaidawa da cewar Annabawan Allah da Manzannin shi sun isar da sakon da ya aikosu da shi.

Ma'aikin Allah  ya dauki tsawan shekaru goma cur yana kira zuwa ga tsantsar tauhidi acikin shekaru ashirin da uku da ya yi yana raye bayan aiko shi a matsayin Manzo, wanda hakan ya ke nuna mana matsayin tauhidi. Ya tura wakilai da yawa wurare daba-daban, misali ya tura Mu'azu Dan Jabal zuwa kasar Yaman yace "Lalle kai zaka je wurin mutanan da su na dauke da littafi, Farkon Abin da za ka kira su akai shi ne su kadaita Allah'' wannan Hadisi Bukhari ya ruwaitoshi. Wannan bayani zai tabbatar mana da cewa lalle ya wajaba mu tsaya domin karanta da karantar da tauhidi, domin da tauhidi ne mutane za su rabauta duniya da lahira, da shi ne kuma za'a sami hadinkan al'ummar musulmi baki dayanta, ta zama 'Tsintsiya madaurinki daya' wanda wannan shi ne fatan ko wanne musulmi.

Ita shirka da Ma'aikin ya fara lissafata acikin jerin gwanon wadannan abubuwa guda bakwai, tana da matukar hadarin gaske, daga cikin manyan hatsarinta wanda ba wanda ya ke so ya afka;

(1)Ita shirka tana tabbatar da mutun cikin azabar Allah har'abada.

(2)Tana sa mutun ya rasa ceton Manzan Allah -tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-.

(3) Tana sa mutum ya yi asarar dinbin ayyukan alheri da ya yi a duniya, kamar taimakawa nakasassu, sadar da zumunci…'.

Saboda haka dukkan wani aikin ibada da Allah da Manzanshi  su ka yi umurni da ayi to mutum ya tabbatar ya yi shi ga Allah kadai kada ya hada kowa tare da Allah. Kuma idan akace Ibada ana nufin 'Gamamman suna ne da ya tara dukkan abinda Allah ya ke so kuma ya yarda da shi, na maganganu da ayyuka na zahiri da na boye.'

To kaga anan muna da nau'ukan ibada masu tarin yawa kamar, Karatun Kur'ani, Sallah, Azumi, Salatin Annabi , Is'tigfari, Hailala, Sada zumunci,Gaida mara lafiya, Yanka, Neman tsari, Neman Agaji, Tawakkali, Kauna, So da sauran su…, wadanda ba'a ambata ba dukkan su na Allah ne Kadai kada mutum ya kuskura ya karkatar da wani nau'i guda zuwa ga wanin Allah, domin Allah yana cewa:

ﭽ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﭼ النساء: ٣٦

Ma’ana: “Ku bautawa Allah (Shi kadai) kada ku hada shi da komai” Suratun-Nisa'i, aya ta 36.

Da kuma fadin Allah madaukaki sarki a cikin Surar ta Nisa’i:

ﭽ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﭼ النساء: ٤٨

Ma’ana: “Lalle Allah baya gafartawa idan aka yi Shirka da shi, kuma yana gafarta abinda bai kai haka ba, dukkan wanda ya yi shirka da Allah to hakika ya kirkiri zunubi mai girma”. Suratun Nisa'I, aya ta: 48.

Wannan yasa Annabawa da Manzanni ba su bari an hada su da Allah wurin bauta ba domin sun san basu can-canta ba, Allah kadai mabuwayi shi ne ya can-canta, Maganganun Annabi Isah –Amincin Allah ya tabbata a gare shi- cikin suratul Ma'idah sun tabbatar da haka, wato inda Allah yake cewa:

ﭽ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﭼ المائدة: ١١٦ - ١١٧

Ma’ana: “Kuma alokacin da Allah ya ce: Ya Isah dan Maryama! Shin kai ne ka ce da mutane; Ku rikeni (ni) da mahaifiyata ababan bauta guda biyu koma bayan Allah? (sai Annabi Isa) ya ce: Tsarki ya tabbata agareka, bai taba kasancewa gareni in fadi abinda ba ni da hakki da shi, in har na fadi hakan hakika ka sani, ka san abinda ke rai na ban san abinda ke ranka ba, lalle kai hakika kai ne masanin abinda ke boye. Ba abinda na fada musu sai dai abinda ka umarce ni da shi, (shi ne kuma) Ku bautawa Ubangijina Ubangijinku”. Suratul Ma’idah, aya ta:116-117.

Hakanan maganganun Ma'aikin Allah  cikin Hadisanshi ingantattu.Karkasuwar Shirka:

Malamai sun yi bayanin cewa shirka ta kasu kashi biyu; Kashi na farko: Shirkar da take futar da mutum daga musulunci (Allah ya Tsare mu), kashi na biyun kuma Shirkar da bata fitar da mutum daga musulunci, Amma tana da mummunan hatsari (Allah ya tsare mu ya kare mu da su baki daya) malamai sukan yi missali kamar:Riya (Yi don a gani) Wannan shi ne mutum ya yi dukkan wata ibata ga Allah amma ya na son agani domin a yaba, ko ace yana da kokari ko ya burge.

Mutum ya san cewa idan ya yi aiki domin a gani ya sani ya yi riya, sai ya nemi Allah ya yafe (Allah ya yafe mana baki daya) wannan yana shafan ayyuka sai dai fatan ki yayewa.

Haka kuma Jiyarwa: Wato mutum ya yi don aji kodai ace yana da murya ko makamantan haka, ko kuma ya yi ibadar shi daga shi sai mahaliccin shi sai yazo yana bada labari, ko ana fira sai aka ganshi yana gyangyadi aka ce mallam lafiya? sai ya kada baki ya ce 'Ai kwana na yi ina nafilfili ko ina karatun Kur'ani ko Zikiri, da sauransu, ko ana zaune yace azuminnan yana ban wahala alhali ba watan Ramadan ake ciki ba, 'ka ji yana cewa ai azumin litinin da alhamis baya wuceni, da dai makamantan su, asani ba muna hukunci akan ayyukan mutane bane amma 'Gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba', saboda haka ayi kokarin an kyautata ayyuka domin Allah.

Anan sauda yawa mutum yakan yi yunkurin zai aikata wani kyakkyawan aiki wanda Allah yake so kuma ya yarda da shi sai ya ji kamar mutane zasu gani su yaba saboda haka sai ya bari ya hakura?, Idan mutum ya samu kanshi cikin irin wannan hali ya aikata aikin da ya ke so ya aikata wannan tsoron da ya ji shi ake bukata, shaidanne ya ke son ya yi amfani da shi domin ya hana shi. Saboda haka kowa ya yi kokari ya ga asalin niyyar sa ta zama domin Allah, sauda yawa magabata sun sha yin Magana akan 'Ikhlasi' wato yi domin Allah, muna fatan Allah ya karba mana.Rantsuwa da wanin Allah. Rantsewa da wanin Allah yana daga cikin dinbin abubuwan da Ma'aikin Allah ya hana, domin babu wani mai girma da za'a rantse da shi In ba Allah ba. Ma'aikin Allah  cewa ya yi: "Duk wanda zai rantse to ya rantse da Allah ko kuma ya yi shiru'' hasali ma duk wanda ya rantse da wanin Allah to rantsuwar bata yi ba (bata kulluba) kuma sai ya yi gaggawar tuba zuwa ga Allah. Amma Allah Sarki mabuwayi mai girma da daukaka mai iko ne akan ya rantse da komai, domin babu wanda zai tambaye Shi, akan haka Allah Ya rantse da rayuwar Manzan Shi Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kuma rantse da rana, wata, hantsi, dare. Da dai suransu.

Awannan takaitaccan bayani da ya gabata mun san hatsarin dake cikin Shirka da Allah wacce Ma'aikin Allah  ya tsoratar da mu ita, da irin alherin da yake cikin Tauhidi.Babi Na Biyu: Sihiri (Asiri)
ASIRI: A yanzu za mu yi bayani akan abu na biyu cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Ya ce suna halakarwa, wannan abukuwa shi ne SIHIRI (ASIRI).

Asiri shi ne abu na biyu da Ma'aiki Allah  ya lissafa cikin abubuwa bakwai masu halakarwa bayan shirka da Allah. Sihiri/Asiri yana daga cikin abinda yake raba bawa da Allah cikin kankanin lokaci, mutum ya dauke dogaron shi da Allah ya sanya shi ga siddabaru ko wani mai siddabaru, wanda hakan zai iya kai mutum ya rasa addinnisa bakidaya.

Idan kana beye da tarihin musulunci ka san yadda Annabi Musa Alaihissalam ya yi fama da masihirtan zamaninsa mabiya Fir'auna, wadanda Fir'aunan ya gayyato daga ko'ina domin su kalubalanci Annabi Musa. Wannan ya nuna lalle Matsafa sun ci karansu ba babbaka a zamanin Fir'auna, amma cikin taimakon Allah alokacin da suka ga Mu'ujizar Annabi Musa suka yi imani da shi sai suka watsar da dukkan kayan tsafe-tsafensu, ba irin barazanar da Fir'auna bai yi musu ba amma suka ce:

ﭽ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﭼ طه: ٧٢Ma’ana: “Ka yi duk abinda zaka yi”. Suratu Taha, aya ta: 72.

Wannan ya nuna mana tarihin matsafa dadadde ne, kuma a har yanzun nan suna nan. Abinda ake so daga dukkan wanda yake musulmi shi ne ya sani Allah ya haramta tsafi/sihiri/asiri/tsubbu/bokanci/duba da dukkanin jinsin wadannan al'amurra, harma ga shi Ma'aikin Allah  ya sanya shi cikin abubuwa bakwai masu halakarwa, Lalle Ma'aikin Allah  ya isar da Manzanci. yana daga ciki halayan matsafa/ masihirta asani 'Tintiran Makaryata ne'.

Daga cikin misalan da suke nuna haka, al'ummar da su ka zo kafin wannan al'ummar ta manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Allah ya ba mu bayanin su a cikin littafinsa mai tsarki Alkur'ani, inda a Suratul-Bakara a aya ta 101 -102 yake bamu labarin wadansu inda yake cewa:

ﭽ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲ ﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﯹ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭼ البقرة: ١٠١ - ١٠٢


Ma’ana: “Kuma alokacin da wani Manzo (Maigirma) ya zo musu daga wurin Allah mai gasgata dukkan abinda yake tare dasu, (Alokacin da wannan manzon ya zo musu) sai wasu daga cikin wadanda aka baiwa littafi sukai watsi da littafin Allah can bayan su kamar kace basu sani ba. Suka bi abinda shaidanu suke karanta musu akan mulkin (Annabi) Sulaimana, Kuma (Annabi) Sulaimana bai kafirci ba, saidai shaidanu ne suka kafirce, (domin) suna koyawa mutane Asiri…''.

Suratul Bakarah, aya ta:101-102


Wannan ya nuna cewa dukkan irin labarinda ake bayarwa na cewa Annabi Sulaiman –Alaihissalam-ya mulki mutane ne da aljanu ta hanyar asiri karyane tsantsa, wadda wadancan shaidanu suka dinga ruruta wutar ta har ya kai aka kirki wadansu hatimai ake sayarwa/bayarwa ga dukkan masu mulki ko masu san mulki wai Hatimin Annabi Sulaiman! Aji tsoron Allah a sani za'a tsaya a gaban Allah ranar kiyama, ko kuma hatimin Annabi Yusufu –Alaihissalam- wai maganin farin jini.

Anan koda ace wani abu ya faru sai wani boka ya ce aje wuri kaza a tona za'a ga abukaza da kaza, kuma aka tona din aka gani, to a sani fa karya ne, domin zai iya tsarawa ya aiki aljanin da suke aiki tare yaje ya aikata hakan sannan yace maka/ki wanene/wance su ka aikata maka/ki.

Abin mamaki da ban takaici shi ne ka ga mutum ya yi karatu digiri na daya koma har ya kai ga digirin-digirgir amma ka ga wani mutum ne yake juya shi, wanda watakila mutumin ka ganshi ba arabi ba boko, ko wani alhaji bai da dama ya sayi wani abu sai ya gayawa wai malaminsa, har abin ya shiga cikin jikin mutane idan Allah ya yi ma ka budi na karin girma ko abin hannu ko ilimi da dai sauran su, sai ka ji ana cewa to fa sai ka tashi tsaye, ko kuma mace ce megidanta zai kara aure, wata kila wanda yake wannan maganar wakiline (agent) na wani boka da su ke hada-hada tare, Allah Ya tsare al'ummar musulmi daga sharrukansu, amin.

Sau dayawa abinda yasa ake cewa ka tashi tsaye wai saboda magabta da mahassada, anan nake cewa addinin musulunci baibarmu haka kara zubeba, ya tsara mana hanyoyin da ake bi don kaucema sharrin masharranta.


Nau'ukan Sihiri:

Sihiri yana da nau'uka iri daban daban da akebi, kuma ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi – ya haramta hakan:

(1) Firaku: Shiri ne n araba miji da matar shi ko mata da mijinta, ta hanyoyi daban-daban. Wani lokacin sai mutum ya ji matar shi tana wari/doyi, ta yi wankan ta sa masa turaran amma baidaina ji ba, wanda yake da ba haka ya ke ji ba. Ko a kashewa miji mazakuta ya ji in ya na dakinta to namiji ya ke, amma idan yana dakin da ba na ta ba, to ba namiji ya ke ba. Duk wani siddabaru da ka yi domin raba ma’aurata to wannan shi ake kira da firaku, Allah madaukakin sarki ya na cewa akan irin barnar da masihirta su ke yi:

ﭽ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭼ البقرة: ١٠٢Ma’ana: “Kuma su na koya daga wurin su abinda su ke raba mutum da matarsa”. Suratul Bakara, aya ta:102.

(2) Canfi: yana cikin irin abinda al'umma ta dade tana ta'amuli da shi a matsayin wata hanya ta samun alhairi ko akasin haka, akan canfa tsuntsu ko kukansa ko mutum ko makaho ko gurgu, Ma'aikin Allah –Tsira da amincin su tabbata a gareshi – ya ce 'Bai daga cikimmu duk wanda ya yi canfi, ko aka camfa shi'.

(3) Zaburar Da Tsuntsaye: shi ma wannan wani camfi ne da ake yi da tsuntsaye, mutum idan zai yi tafiya zai fita da duku-duku zuwa inda bishiyar da tsuntsaye suke taruwa ya raka ihu ta yadda zai tarwatsa su inda suka nufa to ta nan sa'a take, wannan fa tun zamanin jahiliyyah, Allah Ya tsaremu, domin wannan yana bayyanar da haukan mutum a fili.

(4) Zane a kasa: shi ma wannan nau'ine na Sihiri a yi zane akasa domin gano wani alheri ko sharri, wato duba.

(5) Dabo/Rufa ido: su ma waddan nan manya ne a nau'ukan sihiri.

(6) Annamimanci: Shi ma wani nau'i ne na sihiri dubi yadda dauke-dauken maganganu suke canza hakikanin al'amurra ya mai da mai gaskiya makaryaci ko ya maida makaryaci mai gaskiya.

(7) Bokanci: Haka bokanci bai halattaba, kuma bai halatta a je wurin wanda ya ke yi ba.

(8) Duba: Wanda zai duba abinda zai faru nan gaba, yin wannan aiki da zuwa wurin mai wannan aiki bai halatta. Da bokanci da duba abubuwane masu matukar halakarwa, domin yanzu sais u raba mutum da mahaliccin sa.

A hadisin Abuhurairah  Ma'aikin Allah –Tsira da amincin su tabbata a gare shi – Ya ce: ''Duk wanda ya je wajan dan-duba ko boka, ya kuma gasgatashi dangane da abinda ya fada masa, to fa tabbas ya kafircewa duk abinda aka saukarwa (Annabi) Muhammad –Tsira da amincin su tabbata a gareshi –)).

Lalle wannan ya isa halaka, domin akan haka Ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya lissafa shi cikin abubuwa bakwai masu halakarwa.

Hanyoyin Neman Tsari:

Idan aka kallaci hanyoyin neman tsari daga sihiri da masihirta to za'a raba su gida biyu.Hanya Ta Farko: Adunkule wannan hanya ita ce lizimtar dukkanin abubuwan da Allah Malicci Ya yi umarni da ayi daidai gwargwado, kamar tsayar da Sallah akan lokaci a cikin kyakkyawan tsarki, da yawan nafifilin da Shara'a ta zayyana da yawan karatun Al'kur'ani mai girma, ya zamana akullum kana da abinda za ka karanta ba wai sai watan Ramadan ba, da Is'tighfari da kula da zikiran bayan Salloli, da addu'o'in shiga bandaki, domin bandaki yana daga cikin wuraren da suke matattara aljanu, mafi kyawun littafi na zikiri da aka rubuta anan kurkusa shine ‘Hisnul Muslim’ zaka/ki same shi awuraren masu saida littattafai na bakin titi ko na cikin shaguna, an fassarashi zuwa Hausa da Ingilishi.

Hanya Ta Biyu: Kayyadaddiyar addu'a kamar:

(1) Ayatul Kursiyyi, Ma'aikin Allah  Ya ce: “Duk wanda ya karanta ta alokacin da zai kwanta Allah zai sanya mishi mai kula da shi har gari yawaye”. Bukhari ya ruwaito shi, kuma ayar:

ﭽ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰﯱ ﯲ ﯳ ﯴ ﯵﯶ ﯷ ﯸ ﯹﯺ ﯻ ﯼ ﯽ ﯾ ﭼ البقرة: ٢٥٥
(2) Amanar Rasulu (Ayoyi biyun Karshen Suratul Bakara) alokacin da mutum zai kwanta bacci, “Duk wanda ya karanta su sun isar masa”. Bukhari da Muslim suka ruwai to, ga ayoyin:

ﭽ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫﮬ ﮭ ﮮ ﮯﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲ ﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷﯸ ﯹ ﯺ ﯻ ﯼ ﯽ ﯾ ﯿ ﰀﰁ ﰂ ﰃ ﰄ ﰅ ﰆﰇ ﰈ ﰉ ﰊ ﰋ ﰌ ﰍ ﰎ ﭼ البقرة: ٢٨٥ - ٢٨٦

(3) Addu'a ta uku alokaci wanciya bacci ita ce: zaka buda hannayanka biyu, sai ka karanta Kulhuwa sai ka tofa a hannuwannaka, sannan sai ka karan ta Falaki, ita ma ka tofa, sannan sai ka karanta Nasi ita ma ka tofa, sannan sai ka shafo jikinka daga saman (kai) zuwa inda ka tsaya, sannan sai ka maimaita ‘Kulhuwa da Falak da Nas’, kana tofawa a hannayan na ka sannan ka shafa a jiki, sannan sai ka sake maimaitawa, sau uku kenan, ga wadannan surorin:

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭼ

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭼ الإخلاص: ١ - ٤ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭼ

ﭽ ﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭭ ﭮ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﭼ الفلق: ١ - ٥ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭼ

ﭽ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﭼ الناس: ١ - ٦


Dukkan wadannan addu'o'in ana matukar bukatarsu zaka same su cikin wannan littafin na ‘Hisnul Muslim’. Allah ya karemu daga dukkan sharrin masharranta, amin.

Wadannan wadansu hirzine da Ma'aikin Allah –Tsira da amincin su tabbata a gareshi – ya karantar da wannan al'umma tashi, domin matsafa ba irin hanyar da ba za su bi ba domin su ga sun cutar da al'umma.

Wadannan takaitaccan bayani ya nuna yadda Asiri yake halakar da wanda ya yi da wanda ya sa a yi, da kuma yadda ya ke nuna mu'amala da boka ko danduba yana cikin abinda yake warwarewa mutum imaninsa da Allah, domin duk wanda ya yi imani da Allah da Kaddara ba zai aikata wannan danyan aikinba. Allah ya tsaremu, amin.

Babi Na Uku: Kisan Kai
Kisa: A wannan babi za’a yi bayani ne akan abu na uku cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa shi cikin abubuwan da suke halakarwa, wannan abu kuwa shine Kisa.

Allah madaukakin Sarki ya haramta kisa haka kawai ba tare da dalili na shara'a ba, kuma Ya sanya nau'ukan narkon azaba ga dukkan wanada ya aikata kisa.


Karkasuwar Kisankai:

Kashi na Farko: Mutum Ya Kashe Kanshi Da Kanshi.

Allah Madaukakin sarki Yana cewa a cikin littansa Alkur'ani:

ﭽ ﭹ ﭺ ﭻﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﭼ النساء: ٢٩ - ٣٠

Ma’ana: “Kada ku kashe kawunanku, lalle Allah Ya kasance mai rahama ne a gareku. To duk wanda ya aikata haka (ya kashe kanshi) dan kiyayya da zalinci to da sannu zamu konashi da wuta, hakanko ya kasance a wurin Allah abune mai sauki”. Suratun Nisa'I aya ta 29-30.

Ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya ce “Duk wanda ya kashe kanshi da wani abu to da wannan abun za'a azabtar da shi”.

Hakan nan da ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yake cewa:

Duk wanda ya kashe kanshi da guba to zai zo ranar kiyama yana ta hambadar wannan gubar acikin wuta, hakanan duk wannda ya kashe kanshi da wuka zai zo ranar kiyama da wuka a hannunsa yana ta caka wa jikinshi a cikin wuta”.

Ibnu Kasir ya kawo wadannan hadisai alokacin da yake fassara wadancan ayoyin na da suka gabata.

Tabbas wannan yana nuna mana cewa kwata-kwata bai halattaba don mutum ya samu kanshi cikin bakin ciki da damuwa da tashin hankali ya ce zai rataye kanshi kodai a fankar dakinshi ko ya tafi daji ya rataye kanshi a wata bishiya, ko ya fada cikin kogi, ko ya hau katuwar gada ya diro, damadai duk wata da take kisa mace ko namiji, Allah Ya tsaremu baki daya amin.


Shin Ya Hallata Ayi Masa Sallah?

Ya hallata ayi mishi sallah domin bai kafirta ba, saidai malamai da masu fada aji ba za su halarci sallar da binne shi ba, don kada yaba sauran mutane damar aikata irin wannan danyan aiki, amma bai hana su roka mishi gafarar Allah a inda suke tsakaninsu da Allah ba.


Kashi Na Biyu: Kisan Ganganci:

Kisan gangaci shine: “Mutum ya yi nufin kashe wani sannan ya dauki abin da ya ke kisa ya kashe da shi”.

Allah madaukakin Sarki Yana cewa:

ﭽ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﭼ النساء: ٩٣Ma’ana: “Kuma duk wanda ya kashe mumini da gangan to sakamakonsa Jahannama kuma zai dawwama acikinta kuma Allah Ya yi fushi da shi, kuma Ya tsine masa, kuma Ya yi mishi tattalin azaba maigirma.''. Suratun Nisa'i, aya ta:93. (Allah ya tsaremu, amin).
Hukuncin Kisan Ganganci:

irin wanna kisan na ganganci Allah madaukakin sarki ya yi bayaninsa a cikin Alkur'ani mai girma inda Allah Ya ke cewa a Suratul-Bakara:

ﭽ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﭼ البقرة: ١٧٨

Ma’ana: “Ya wadanda suka yi Imani!, an wajabta muku ramuwa dan gane da wadanda aka kashe”. Bakara, ayata:178.

Haka kuma Allah Ya ce:

ﭽ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﭼ المائدة: ٤٥

Ma’ana: “Kuma mun wajabtamusu acikinta (Attaura) Lalle ana kashe rai idan ran nan ta kashe (wata rai)”. Suratul Ma'idah, aya ta: 45.
Ma'anar Kisasi: (wato ramuwa) shine yadda wanda aka kashe ya dandani dacin mutuwa to shima wanda ya yi kisan ya dandana, irin wannan hukuncin shi zai tabbatar da zaman lafiya, domin duk mutumin da yasan indai ya kashe to tabbas za'a kashe shi ko shi waye to lalle zai shiga taitayinsa, wanda hakan zai sanya rayuwa ta aminci tsakanin al'umma. Amma farfagandar da ake yi da sunan kare hakkin dan'adam na cewa shara'ar musulunci ta tsaurara domin bata kula da hakkin dan'adam ba, irin wannan maganar tana nuna jahiltar menene hakkin dan’adam?! domin ai shi ma wanda aka kashe dan'adamne kuma yana da hakki, yanzu dan an karbar masa hakkinsa sai ace donme?.

Yafiya:

Idan 'yan'uwan wanda aka kashe suka ce sun yafe, to shikenan ba za'a kashe wanda ya yi kisanba sai ya bada diyya ga su 'yan'uwan wanda aka kashedin, sannan kuma ya yi azumi sittin ajere.Kashi Na Uku: Kisan Kuskure:

Kisan kuskure shi ne: “Kisan da aka yi ba tare da anyi nufiba”. kamar maharbi ya hangi dabba bayan ya kammala shiri ya sakar mata kibiya kawai sai kibiyar nan ta wuce ta sami wani can daban yana noma ko ya zo wucewa.Hukuncin Kisan Kuskure:

Hukuncin kisan kuskure shine 'Za'a bayar da diyya ga dangin wanda aka kashe, sannan za'a 'yanta baiwa/bawa mummunai, idan ba'a samu ba sai ayi azumin kwanaki sittin ajere, Allah Ya karemu, amin.

  1   2   3


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©azrefs.org 2016
rəhbərliyinə müraciət

    Ana səhifə